Labaran Ƙarya Na Ƙoƙarin Tarwatsa Ƙasar Nan – Hukumar DSS

125

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta koka da yadda ake samun karuwar labaran karya ta kafar intanet, wanda ka iya ingiza al’umma su tayar da rikici.


Hukumar ta yi wannan bayanin ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun jami’in yada labaran ta, Dr. Peter Afunanya, biyo bayan illar da ta hango kan illar da wannan dabi’ar ka iya haifarwa a kasar nan.


Afunanya ya jaddada jan hankalin da hukumar ta yi tun da farko kan shirin wasu bata garin kungiyoyi na hargitsa tsaron kasar, inda ya ce sun kudiri aniyar amfani da banbance-banbancen siyasa da sauran matsalolin da suka addabi kasar a ciki da wajen ta don bata ta.


A cewar sa, bata garin sun kirkiro labarai masu cike da karairayi don cimma munanan muradinsu na ganin kasar ta barke da rikicin da ke da nasaba da kabilanci da addini wadanda ka iya fitar da kasar daga hayyacinta.


Jami’in ya ce hukumar tsaro ta DSS za ta ci gaba da aiki tukuru don jaddada zaman lafiya tare da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar kasar, sannan ya yi tir da halin rashin kishin kasa da wasu bijirarrun ‘yan kasar ke nunawa, inda yi kashedin cewa doka zata yi halinta a kansu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan