Shi ne gwamnan Kano mafi gajartar zango a tarihin gwamnonin jihar Kano, ya zauna a wannan kujera na tsawon watanni biyu kawai. Shi mutumin unguwar Bakin Zuwo ne, wanda daga sunan unguwar ne ma ya samu Laƙabinsa na ‘Sabo Bakin Zuwo’. Wannan unguwa tana nan a cikin ƙwaryar birnin Kano.
An haife shi a wannan unguwa ta Bakin Zuwo a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1934.
Duk da cewa bai yi nasarar fara karatun zamani tun yana ƙarami ba, ya fara ne da karatun Ƙur’ani a nan unguwar tasu ta Bakin Zuwo. Ya fara karatunsa na Zamani a makarantar Shahuci, inda ya halarci darrusan yamma (Karatun manya na yaƙi da jahilci). Daga baya ya shiga makarantar ‘Ibo (Igbo) Union School’ da ke Sabon Garin Kano.
Sannan kuma ya zarce zuwa makarantar mulki ta Zariya (Zaria Administration Institute). Ya zama shugaban ƙungiyar ‘yankasuwa (United Labour Congress) reshen jahar Kano . Sannan ya zama mataimakin shugaba, na ƙasa, na wannan ƙungiyar. Ya yi aiki tare da kwamatin tantance masu karɓar bashi na jahar Kano (State’s Rent Assesment Committee). Sannan ya zama shugaban Hukumar Ƙayyade Farashi (Chairman Price Control Board). Sannan ya zama shugaban hukumar tsaftace kamfanoni (Chairman Indutrial Council Safety). Haka nan kuma ya taɓa zama shugaban Ƙungiyar ‘Yan’Dambe ta jahar Kano (State’s Ameteur Boxing Association).
Alhaji Sabo bakin Zuwo ya zama gwamnan jihar Kano ƙarƙashin tutar jama’iyyar PRP, bayan lashe zaɓen da aka gudanar a watan Agusta na shekarar 1983.
Duk da wannan ƙarancin lokaci da ya yi a kan kujerar gwamna, bai rasa abin ambato da ya bari ba, ya samu nasarar mayar da sinimar falas (Palace Cinema) da ke Unguwarsu ta Bakin Zuwo zuwa asibitin haihuwa (meternity home). Ana kiran wannan asibiti da sunansa
Sai dai sojoji sun yi juyin mulki idan su ka kifar da gwamnatin farar hula, wanda hakan ya kawo manjo janar Muhammadu Buhari karagar mulki.
Bayan juyin mulkin da soji su ka yi wanda ya kawo ƙarshen mulkin farar hula, gwamnatin sojin ƙarƙashin mulkin shugaba Buhari ta kama marigayi Sabo Bakin Zuwo tare da ɗaure shi shekaru 300 a gidan yari, bisa ikirarin samun zunzurutun kuɗi sama da naira miliyan 3 ajiye a gidansa.
Sai dai kuma gwamnatin Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ta sake shi tare da sauran ƴan siyasar da gwamnatin Buhari ta kama, bayan da aka same su babu wani laifi a tare da su.
[…] Muƙalar Da Ta GabataMarigayi Sabo Bakin Zuwo: Gwamnan Da Aka Ɗaure Shekaru 300 A Gidan Yari […]