Ƴan Bindigar Katsina Sun Saki Mata 10 A Cigaba Da Sulhu

97

A cigaba da sasantawar da ake yi da ƴan bindiga a jihar Katsina, wadanda su ka yi garkuwa da mutane da dama, sun sake sako mutane a karo na biyu. Rukunin na 2 da ‘yan bindigar suka sako, sun kunshi mata 10 da wani jinjiri, wanda ya bada jimlar mutane 16, idan aka hada da guda 5 da aka sako ranar Lahadin da ta gabata.


Wannan ya biyo bayan rangadin da gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya kwashe tsawon mako daya ya na yi, domin tattaunawa da kuma yin sulhu da ‘yan bidigar da ke tada kayar baya a jihar, wadanda su ma aka saki mutanensu kusan 9 da ake tsare da su.


Ayyukan ƴan tada kayar baya da suka hada da kai hare-hare, da kisan jama’a da ma sace su domin karbar kudin fansa, sun ta’azzara sosai a jihar Katsina, jim kadan bayan da rahotanni suka nuna cewa an soma samun zaman lafiya a makwabciyarta jihar Zamfara, sakamakon fito da tsarin sulhu da ‘yan tada kayar baya.


Wannan ya sa jihar ta Katsina rungumar tsarin na sulhu, duk da yake gwamna Masari ya ce jihar ce ta soma gudanar da tsarin.


To sai dai tuni da wasu manazarta sha’anin tsaro suke bayyana tababa akan tabbacin samun nasarar tsarin na sulhu, a zaman hanyar kawar da ayyukan ‘yan bindigar, to amma Sakataren gwamnatin jihar ta Katsina, Mustafa Muhammad Inuwa, wanda shine ke jagorancin shirin na sulhu a jihar, yana da ra’ayi banban.


Har kawo yanzu dai, akwai sauran mutane kusan 18 da ba a sako ba, daga cikin mutane 29 da ‘yan bindigar su ka yi awon gaba da su a garin Shimfida kadai, a wani hari da suka kai makwanni biyu da suka gabata, kazalika da wasu kuma da aka ce an kama a wasu garuruwan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan