An kama sarkin Wakar Sarkin Kano

178

Yawaitar kama mawaka da sauran yan adawa ya fara kaiwa intaha a Kano, yanzun nan, aka je har gidan Nazir Sarkin wakar sarkin Kano, aka kama shi kuma an je neman beli ance sai dai gobe a dawo.

A kwanakin baya ma dai an kama Oscar 442 wani Dirakta a Kannywood, haka kuma rahotanni na cewar akwai mutanen da aka lissafa za a kama su daya bayan daya, saboda wakokin su, suna marawa akidar Kwankwasiya baya.

A Kamun farko dai an fara ne da Sadeek Zazzabi wanda har sai da ya dangana da kai shi kurku, daga bisani aka kama Sunusi Ocar 442, yanzu kuma gashi an kama sarkin Wakar Sarkin Kano.

Har ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan laifin da mawakan da yan fim ke aikatawa, amma sai dai wasu na gani kamar bita da kulli ne ga wadanda basa goyon bayan gwamna mai ci Abdullhai Umar Ganduje.

A bangare guda kuma Hukamar tace Finafinan ta gaza samar da gasasshen dalilin kamen yan masana’antar Nishaɗantarwar.

Nasir Salisu Zango ɗan Jarida a Kano ne dai ya fara wallafa labarin a shafinsa na sada Zumunta.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan