Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Atiku

132

A ranar Larabar nan ne Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP da jam’iyyar suka shigar, inda suke buƙatar Kotun ta soke nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2019.

Kotun, a wani hukunci da gaba ɗaya alƙalan suka amince da shi, ta yanke hukuncin cewa Atiku da PDP sun kasa kawo hujjojin da suke so a soke nasarar Shugaba Buhari da su.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan