Miliyoyin Al’ummar Ƙasar Nan Na Cikin Wahala Saboda Matsalar Cin Hanci -Buhari

23

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa akan yadda rashawa da cin hanci su ke ƙara kawo naƙasu akan cigaban ƙasar nan.


Shugaba Buhari ya ce matsalar cin hanci da rashawa ne ya jefa miliyoyin ƴan ƙasar nan cikin halin ni ƴa su.


Ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa shi ne babbar matsala da ake fama da ita a dukkanin matakan gwamnati, wanda hakan kan kawo cikas ga haɓakar tattalin arzikin ƙasar nan.


Shugaban ya yi wannan furucin ne a gurin taron ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta ƙasa karo na 49 mai taken gina ƙasa akan tafarkin cigaba mai ɗorewa.


“Daga yanzu ina buƙatar ku din ga yiwa cin hanci da rashawa kallon wani abu da kan jefa al’umma cikin halin ƙaƙanikayi, domin matsalar sa ce ta jefa miliyoyin al’ummar ƙasar nan cikin halin tsanani, rashin lafiya tare da gazawa” In ji shugaba Buhari.


Shugaban wanda ya samu wakilcin babban sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha, ya ƙara da cewa yaƙin da gwamnatinmu ta ke akan cin hanci da rashawa da gaske ake yi, domin a samar da nagartacciyar ƙasa.


“Yaƙin da mu ke akan cin hanci da rasahawa da gaske gwamnatinmu ta ke, domin hakan ne kawai zai samar da ƙasa wacce za ta ɗore”


A nasa ɓangaren shugaban hukumar ƙwararrun akantoci ta ƙasa Mista Nnamdi Okwuadigbo ya jinjinawa ƙudurin hukumar wajen samar da cigaba da bunƙasar tattalin arzikin ƙasar nan. Ya ce lokaci ya yi da ya kamata da al’ummar ƙasar nan za su dawo da martabar sunan ƙasar nan a idon ƙasashen duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan