Ya Zama Dole Mu Ɗaukaka Ƙara- Atiku

179

Mike Ozekhome, ɗaya daga cikin lauyoyin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashi takobin ƙalubalantar hukuncin da Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke.

A ranar Larabar nan ne Kotun ta yi watsi da ƙarar da PDP da Atiku suka shigar gabanta, inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaɓen Shugaban Ƙasa na 23 ga watan Fabrairu.

Da suke yanke hukunci, gungun alƙalai biyar waɗanda Mai Shari’a Mohammed Garba ya jagoranta, sun yi watsi da ƙarar Atiku saboda gaza gamsar Kotun da ƙwararan hujjoji.

Mai Shari’a Garba ya bayyana cewa ƙarar Atiku ta kasa nuna wata hujja da za ta nuna cewa ba a gudanar da zaɓen 2019 ba kamar yadda Dokar Zaɓe ta tanada.

Amma, Mista Ozekhome ya ce wanda yake wakilta zai ƙalubalanci wannan hukunci.

“Cewa za mu ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli ai tabbas ne kamar yadda mutuwa take tabbas”, in ji Mista Ozekhome.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan