An Kai Hari Akan Masallacin Juma’ah A Ƙasar Afirka Ta Kudu

254

An kai wa Masallacin Juma’a na biyu hari a cikin mako guda a ƙasar Afirka ta Kudu.


Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa wasu da ba’a san ko su waye ba ne suka kai hari da harasan wuta kan Masallacin Juma’a na Himayatul Islam dake yankin Hillbrow na garin Johannesburg.


Wani ɓangare na Masallacin Juma’ar ya kone.
Masallacin Juma’ar na Himayatul Islam na a yankin da a ‘yan kwanakin nan ake kai wa ‘yan kasashen waje hare-hare a cikinsu.


Ƴan sanda da suka fara gudanar da bincike sun kama mutane 2.


A ranar Larabar da ta gabata an kai hari kan Masallacin Juma’a na Katlehong dake Johannesburg.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan