Shan Ruwan Sanyi Yana Sakawa A Tsufa Da Wuri – Bincike

582
Glass and jug of ice water

Wani likitan yara dake aiki a Benin babban birnin jihar Edo mai suna Ovo Ogbinaka ya ce yawaita shan ruwan sanyi na cutar da kiwon lafiyar mutum.


A hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin labarai na ƙasa NAN a garin Benin, Ovo Ogbinaka ya ce ya gano haka ne a binciken da yayi game shan ruwan sanyi da illar da ke tattare da shi.


Ya ce sakamakon binciken ya nuna cewa yawan shan ruwan sanyi na sa mutum ya tsufa da wuri sannan kamuwa da cututtukan dake kama hakarkari da zuciya.


Kuma ba’a iya gane illar shan ruwan sanyi sai mutum ya fara tsufa.

Ya ce idan har ya kama a sha ruwa mai sanyi kamata ya yi a rage sanyin ruwan kafin a sha domin rashin yin haka ne ke cutar da kiwon lafiyar mutum.

Sauran illolin dake tattare da shan ruwan sanyi sun haɗa da:

  1. Shan ruwan sanyi na kawo mura,tari da toshewar murya.
  2. Ya hana narkar da abinci a cikin mutum.
  3. Yana daskarar da jijiyoyin jiki wanda hakan ke hana jini gudana.
  4. Shan ruwan sanyi na haddasa taruwar kitse a kodar mutum.
  5. Yana kuma lalata hanji da hakan ke sa a kamuwa da ciwon daji.
  6. Shan ruwan sanyi na sa kirji ya yi ta ciwo.
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan