Zakara Ya Cinye Ɗan Kunnen Zinare

242

A kasar Habasha, wani zakara ya sha wuka bayan cinyewa wata mace dan kunnenta na zinare da yayi.
An tilasta ma ta sayen zakaran domin ta iya tsira da dan kunnen nata.
Matar mai suna Hachaltu Bedira ta je cin kasuwar Woliso, a jihar Oromia domin sayar da kajinta a daidai lokacin da ake gab da fara bikin sabuwar shekarar kasar.
Amma ba ta tafi kasuwar da niyyar sayo zakara ba, kuma zakaran na wani dan kasuwa ne da shi ma ya zo cin kasuwar.
Sai dai an shiga rudani a lokacin da zakaran ya tsere daga hannun ubangidansa tare da fizge dan kunnen zinaren na Hachaltu tare da hadiye shi nan take.
Dole ‘yan sanda suka shiga batun, tare da cafke zakaran da ya tada husumar bayan da lamura suka dagule.
Babban jami’in ‘yan sanda Tadesse Bedada ya shaidawa BBC cewa bayan dogon nazari sun gano za a iya warware matsalar ne kawai tsakanin ‘yan kasuwar biyu.
Daga karshe dole mis Hachaltu ta sayi zakaran dala 5, kwatankwacin Naira 1,790. Wanda hakan ya sabawa ainihin kudin da ake saida tirkeken zakara kamarsa a kasuwar.
Mai zakaran ya amince da farashin domin rage asara, wanda hakan shi ne mafita ga matar domin ta samu a yanka shi kana ta ciro dan kunnenta na zinare.
Jami’in ya kara da cewa a lokacin da suke tsare da zakaran, sun lura yana ta raba idanu, domin gano abubuwa masu launin zinare domin ya hadiye.

Rahoton BBC Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan