An Gano Gawar Wani Bayan Shekaru 20 Ta Google

181

An gano gawar mutumin da ya bata shekaru 22 da suka gabata a Florida ta hanyar amfani da taswirar Google.
Tun a watan Nuwambar shekarar 1997 aka kai rahoton bacewar William Moldt daga Lantana a Florida.
Mai shekara 40 a duniya, ya fita shakatawa gidan casu da daddare amma kuma sai bai koma gida ba.
‘Yan sanda sun fara gudanar da binciken bacewarsa a lokacin amma daga bisani batun ya bi shanun sarki.
Amma a ranar 28 gawa Agusta da ya wuce, aka kira ‘yan sanda kan an gano wata mota a cikin ruwa a yankin Moon Bay Circle a Wellington.
A lokacin da aka fito da ita daga kududdufin., sai aka ga kwarangwal din mutum a ciki. Mako guda bayan nan aka gano kwarangwal din Mista Moldt ne bayan gudanar da bincike.
Wani mutum ya gano motar ne ta hanyar amfani da taswirar Google da ke nuna inda mota ta ke kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.
Mutumin ya yi gaggawar shaidawa ‘yan sanda akwai mota a cikin ruwan da ke Moon Bay cirle, bayan amfani da dan karamin jirgi maras matuki na fasaha.
Wani rahoto da kamfanin fasaha na Charley Project ya wallafa, ya ce google ya nuna motar muraran tamkar ta na waje kamar yadda hotunan tauraron dan adam ya nuna tun a shekarar 2007, sai dai kamar babu wanda ya damu ya duba har sai wannan shekarar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Palm Beach County ta shaidawa BBC cewa su na kyautata zaton mota ta kwacewa mamacin ne a lokacin da ya fada ruwan.
Theresa Baebera ta kara da cewa a lokacin da suke gudanar da bincike kan batansa, babu wata shaida da ta nuna akwai mota a cikin kududdufin.
‘Kai tsaye babu wanda zai fadi ainahin abin da ya faru tsahon shekarun nan, abin da muka sa ni shi ne Mista Moldt ya bata, a halin yanzu an gano shi”.

BBC Hausa

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan