D’Tigers Sun Dawo Gida Najeriya

215

Kungiyar kwallon Kwando ta bangaren maza ta kasar nan wato D’Tigers sun dawo gida Najeriya daga can kasar China.

Sun dawo gida ne a jiya Alhamis da rana kenan karkashin jagorancin mai horas wa Alex Nwora inda suka sauka a filin saukar jirage na Murtala Mohammed.

Najeriya dai sun fafata wasannin gasar cin kofin duniya da kasar China take karbar bakunci inda Najeriya ta fafata da kasashen Russia da Argentina da kuma Korea ta Kudu.

Saidai a wasan farko dana biyu Najeriya sunyi rashin nasara a hannun kasashen Russia da Argentina.

Amma sakamakon nasarar da Najeriya ta samu a kan kasar Korea ta Kudu ta sami tikitin buga gasar Olympic da za ayi a Tokyo a 2020.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan