Ya Kamata A Samar Da Abubuwa 8 Kafin Karin Harajin VAT – Bello Sharada

148

Za a koma hutu na Majalisar dattijai da tarayya a satin gobe. Ministar kudi da kasafi Zainab Shamsuna Ahmed, za ta mika wa majalisa kundin kasafin 2020.

A shirin da gwamnati take da shi, shi ne na a kara harajin VAT daga kashi biyar zuwa kashi 7.2 Ita gwamnati tana ta kokarin kara samun kudaden shiga da kashewa, saboda bashin da ake ci a ciki da wajen kasa kullum ninkawa yake yi.

A matsayina na san jam’iyyar APC mai burin ganin ta yi nasara, in gwamnatinmu ta shugaban kasa Muhammad Buhari tana ganin dole sai dai a bi hanyar kara VAT, ina rokonku don Allah ku bari nan da shekara TA 2023:

Na daya: Ku bamu wutar lantarki wadatacciyya, ba yankewa, ku saka mana mita a ko ina, ku bamu farashin da duk duniya take amfani da shi

Na biyu: Ku inganta tsaro a daina kashe mutane barkatai, ku samar da kwanciyar hankali a daina kwana cikin FARAGABA.

Na uku: Ku dauki matakai masu kwari na toshe hanyar da manyan ma’aikata da manyan jami’an tsaro da yan siyasa suke kwashe kudin tafiyar da mulki

Na hudu: Ku baiwa manoma taki da sauki, ku sauya fasalin noman ya koma na zamani, a baiwa manomin gaske layin jari da tallafi na gaske.

Na biyar: Ku mayar da duk wani maganin maleriya kyauta kamar yadda na cutar Poliyo da tarin shika yake a ko ina sadaka

Na shida: Ku gyara ilimi da harkar lafiya da ruwa, daga kan shugaban kasa Muhammad Buhari har zuwa kowane jami’i da su da ‘ya’yansu su rika karatu da ganin likita a Najeriya

Na bakwai: A inganta layin dogo a manyan birane, shi kuma manyan titunan jiha da tarayya a mayar da su na kwarai don a rage halakar da rayukan jama’a

Na takwas: Ku dawo mana da litar man fetur naira 87
Duk kasashen da kuke cewa VAT dinsu yafi namu kauri, to su sun wuce wadannan abubuwan guda takwas

IDAN KUKA YI HAKA BA SAI KUN KARA MANA ALBASHI BA, SANNAN KUMA MUN YARDA KU KARA MANA HARAJIN VAT 10%

Don Allah yan Majalisarmu ga kukanmu ku gaya musu in kun dawo daga hutu

Bello Muhammad Sharaɗa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan