Za’a Saka Gawar Robert Mugabe A Akwatin Naira Biliyan 17

44

Akwatin Gawar da za’a saka tsohon shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe Ya Laƙume naira biliyan 17.


Akwatin gawar dai an kera shi tare da saka masa wasu na’urorin zamani hadi da wata kwamfuta a jikinsa wadda idan iyalinsa sun buƙaci ganinsa za su iya danna wani madanni a jikin wayar tafi da gidanka da aka hadata da akwatin gawar a duk lokacin da suka bukaci hakan.


Daga waje akwatin gawar an kawata shi da wani farin jauhari da madaukai masu daukar hankali.


Da suke bayani wasu turawan Birtaniya da suka kera akwatin suka ce, “akwatin na dauke da wani sinadari da ke hana gawa lalacewa na tsawon shekara 10”.


Bayan nan kuma duk wanda aka yarjewa shima zai iya ganin gawar Mugabe ta hanyar dannan madannin na’urar da aka hada ta da akwatin gawar ko da kuwa ba ahalinsa ba ne inji turawan da suka hada akwatin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan