Bani Da Niyyar Jefe Ƴan Ƙasar Nan A Cikin Wahala – Shugaba Buhari

128

Bayan da Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙara harajin VAT daga kashi 5 zuwa sama da kashi 7 akan kayayyakin da jama’a ke saye a fadin ƙasar, nan shugaban ƙasa

Muhammadu Buhari ya bayyana cewar bashi da aniyar jefa yan kasar nan a cikin kuncin rayuwa.


Shugabancin Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta TUC, inda yake cewa gwamnatin zata cigaba da lalubo hanyar saukakawa jama’ar ƙasar nan halin ƙunci da matsi da su ke ciki.


Shugaban ya jaddada aniyar gwamnatin sa na aiwatar da shirin karin sabon albashi. Sai dai har kawo yanzu babu wata jiha da ta fara aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan