Home / Wasanni / Enyimba Suntashi Wasa Kunnen Doki Da Al-Hilal

Enyimba Suntashi Wasa Kunnen Doki Da Al-Hilal

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da suke wakiltar Najeriya a gasar zakarun Afrika a kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 sun buga kunnen doki a wasan farko da suka kara da kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal ta kasar Sudan.

An tashi wasa babu ci a filin wasan na Enyimba dake garin Aba.

Tun a mintina na 20 da fara wasan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal Hamid Nasir yasami katin kora daga fili wato red card.

Enyimba dai wannan shine wasansu na farko a gida da akabar magoya baya suka shiga filin wasa bayan hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta janye takunkumin data sakawa Enyimba na buga wasa a gida batare da ‘yan kallo ba inda ko wasansu na makonnin baya dasuka buga babu magoya baya.

‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Enyimba sun sami damar jefa kwallaye kamar Nelson Ogbonnaya da Reuben Bala Austin da kuma Okorom amma duk sun kasa jefa kwallo.

‘yan wasan kungiyar kwallon kafan ta Enyimba karkashin mai horas wa Usman Abdallah sun mamaye wasan tun daga farko har karshe amma basuyi nasara ba.

Ayanzu dai nan gaba za a buga wasa na biyu a kasar Sudan tsakanin Al-Hilal da Enyimba.

About Suraj Naiya Kudiddifawa

Check Also

Aubameyang ya kamu da cutar Maleria

Sai dai Har ya zuwa yanzu Arteta bai iya ba da sanarwar ranar dawowar ɗan wasan gaban ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *