Hafsat Ganduje Ta Zama Farfesa

153

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Maryam Abacha da ke jamhuriyar Nijar ta baiwa mai ɗakin gwamnan jihar Kano Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje matsayin mataimakiyar shehin malami wato asoshiyet Farfesa, akan harkokin gudanarwa da tsare-tsare.


Cikin wata sanarwa da hukumar jami’ar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ta bayyana Dakta Hafsat Ganduje a matsayin wacce ta bada gudunmawa a wannan bangare mai tarin yawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa matsayin na Dakta Hafsat Ganduje ya fara ne tun daga rana 14 ga watan Agustan da ya gabata.


Tun da farko dai Dakta Hafsat Ganduje malama ce a tsangayar ilimi ta jami’ar Bayero da ke Kano, wacce ta ke da matakin karatun digirin digirgir wato Dakta akan harkokin gudanarwa da tsare-tsare.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan