Home / Labarai / Ƙasar Afirka Ta Kudu Ta Nemi Gafarar Najeriya Akan Abin Da Ya Faru

Ƙasar Afirka Ta Kudu Ta Nemi Gafarar Najeriya Akan Abin Da Ya Faru

Ƙasa Afirka ta Kudu ta nemi gafarar ƙasar nan akan hare-haren kin jinin bakin da aka kai wa al’ummar ƙasar nan da ke zaune a kasar Afrika ta Kudu.
Jakada na musamman na gwamnatin Afirka ta Kudu, Jeff Radebe, ya gabatar da takardar neman afuwar a madadin Shugaba Cyril Ramaphosa, a wata ganawa da yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.
Da alamu gwamnatin Afirka ta Kudu na kokarin kyautata alakarta da sauran kasashen Afirkan wadanda hare-haren kin jinin baki a Afrika ta Kudun ya shafa.
Jami’in na Afirka ta Kudu, ya shaida wa Shugaba Buhari a Abuja cewa gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da aka samu, kuma ya ce tana daukar kwararan matakai.
A yayin da Afirka ta Kudu ta dauki wannan mataki, ita kuma gwamnatin tarayya na ci gaba da kwashe ‘yan kasar nan daga Afirka ta Kudu.
Ana sa ran isowar wani rukunin al’ummar ƙasar guda 319 daga Afirka ta Kudu a filin jirgin sama da ke Legas a ranar Talata.
Sai dai Shugaba Buhari ya tabbatar wa jami’in cewa za a kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *