Ministan wasanni da matasa na kasar nan wato Sunday Dare ya bayyana cewar yana da tabbacin Thomas Dennerby zaidawo yaci gaba da horas da kungiyar kwallon kafa ta bangaren mata ta kasar nan wato Super Falcons.
A jiya dai Litinin mai horas war ya bayyana aniyarsa ta ajiye aiki inda ya mika takardar ajiye aiki ga hukumar kwallon kafa ta kasar nan inda ya bayyana cewar wasu daga cikin mutane na hukumar basu yaba kokarinsa ba.

Ministan wasanni ya bayyana cewa a shafinsa na Twitter yana bibiyar abin dayasa Dennerby ya ajiye aikinsa a matsayinsa na mai horas wa, inda yace zaiyi duk mai yiwuwa domin Thomas Dennerby ya dawo aikinsa na horas wa.
Turawa Abokai