Fasakwaurin Shinkafa Haramun Ne – Sheikh Yasir Ramadan Gwale

233

Sumogal din shinkafa da ake yi da babura ko fasakwaurinta daga kan iyakokin Nijeriya zuwa cikin gida Haramun, kamar yadda hukumar dake kula da wannan janibi ta sanar. Mutane da yawa na sukar wannan lamari, watakila bisa son rai ko kuma bisa jahilci.

Hakikanin gaskiya yana da kyau mutane su fahimci cewar, manufofin wannan gwamnatin inganta tare da habakar harkar noma musamman na shinkafa, domin manoman shinkafa na gida su samu arziki, ‘yan Najeriya su ciyar da ‘yan Najeriya da shinkafar da aka noma a cikin gida.

Wannan na daga cikin manufofin Gwamnatin Buhari kan bunkasa harkokin noma a Najeriya. Wannan ya sanya hukumar kwastan ta kasa sanya dokoki da ka’idoji kan batun shigo da shinkafa zuwa Najeriya daga kasashen waje.

Hukumar kwastan, tace yin sumoga ko fasakwaurin shinkafa ta kan iyakoki haramun ne, saboda hujjojin da shugaban hukumar Hameed Ali ya bayar, domin kudin da gwamnati ya kamata ta samu na harkar futo, anyi mata asararsu, sannan an shigo da abinda ake zargi yana dauke da guba.

Na farko ita wannan shinkafa da ake shigo da ita Najeriya ta barauniyar hanya, dauke take da guba, domin kafin isowarta Najeriya, an zuba mata sinadarai iri iri wanda zasu hanata rubewa ko lalacewa, saboda warin ruwan teku da ruma da kuma kumewa, wanda binciken hukumar kwastan ya tabbatar da cewar wannan shinkafa mai dauke da wadannan sinadarai tana cutarwa ta hanyar sanyawa mutane ciwon kansa.

Ciwon kansa ko sankara, ba ciwo bane da ake dauka nan take, watakila sai bayan wasu shekaru ciwon ke bayyana a jikin masu dauke da shi. Da wannan dalili da ma wasu, hukumar kwastan tace, duk wanda zai yi kasuwancin shigo da shinkafar waje zuwa Najeriya, to, ya shigo da ita ta hanayoyin da suka dace, domin a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da inganci da kuma lafiyarta. To meye laifin hakan?

Mu ‘yan Najeriya muna da al’adar rashin girmama duk abinda muke da shi. Tayaya manomanmu zasu samu cigaba a harkar noman shinkafa alhali muna kaucewa sayan ‘yar gida muna cin wadda ake shigo da ita daga waje wadda ke dauke da sinadaran da ka iya illata jiki?

Ba daidai bane, mutane su dinga wasa da ratuwarsu, akan dan abinda za a basu in sun yi sumoga din shinkafa daga kan iyakokin da aka rufe zuwa gida Najeriya. Gwamnati dole ta karewa al’umma jini da dukiya da kuma mutuncinsu.

Me yasa masu kasuwancin shinkafa suke son lallai sai dai su shigo da ita ta barauniyar hanya, ta hanyar yin sumoga ko fasakwaurinta? Alhali Kuwa akwai yadda zasu iya shigo da ita a bisa tanade tanaden hukuma, ta anyar mfania da gabar tekun ad gwamnati ta ware domin yin harkar futo.

Yana da kyau ‘yan Najeriya su yiwa kansu tambayar me yasa ake sumogal din shinkafa indai sahihiya ce, kuma halastaccen kasuwanci mutane suke yi na sayar da shinkafar? Indai sun tabbatar shinkafar bata dauke da guba, me yasa ake tsoron shigo da ita ta gabar teku?

Ya danganta, ko dai ace zata yi tsada idan aka shigo da ita ta kan iyakokin Najeriya da aka tanadar wato teku, wannan kuma ba wani abin damuwa bane, domin wanda ba shi da ikon cin shinkafar da aka shigo da ita daga waje saboda tsada, yana iya sayan wadda aka noma ta a Najeriya, kuma wannan shi zai baiwa manoman shinkafa na gida damar bunkasa harkar noman shinkafar gida.

Babu wata gwamnati da ta san abinda take yi, zata yadda a dinga jidar dala daga Nijeriya, ana zuwa wasu kasashe ana azurta manoman shinkafar can kasashen, suna bamu shinkafar da aka cika ta da sindaran da zasu illata lafiya, alhali za a iya samar da shinkafar a gida Nijeriya mai tsafta da inganci, mara cutarwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan