Yau Za a Fara Gasar Zakarun Nahiyar Turai

200

A yau Talata 17 ga watan Satumba za a fara gasar zakarun nahiyar turai wato sabuwar kaka ta 2019 zuwa 2020.

A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ce ta zamo zakara inda ta lashe gasar karo na 6.

Gasar zakarun nahiyar turai gasace mai dimbin tarihi wanda tun tana European Cup aka sauya mata suna ta koma gasar zakarun turai wato Uefa Champions League.

Daga cikin wasannin daza a kara a yau da gobe akwai wasanni masu zafi kuma masu daukan hankali kamar haka:

Brussia Dortmund da Barcelona.

Chelsea da Valencia.

PSG da Real Madrid.

Napoli da Liverpool.

Athletico Madrid da Juventus.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan