Gwamna Ganduje Ya Buɗe Gidan Mai Irinsa Na Farko A Arewacin Najeriya

254

A jiya talata gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya buɗe wani katafareren gidan mai da babu kamar sa a faɗin arewacin ƙasar nan.
Gidan man wanda fitaccen matashin ɗan kasuwar man nan na ƙasa kuma shugaban rukunin gidajen mai na SALBAS OIL AND GAS, wato Alh. Sale Baba ya gina shi a garin Tamburawa da ke kan hanyar Kano zuwa Zaria
Gidan man zai kasance yana aiki tsahon sa’o’i ashirin da huɗu ba tare da tsayawa ba. Haka kuma yana ɗauke da ababen buƙatun al’umma tare da wadataccen tsaro.
Akwai kuma shagon sayar da magunguna na zamani, na’u’rori masu kwalkwalwa domin ziyartar yanar gizo a kowanne lokaci, kayan masarufi domin iyali da sauran ababen more rayuwa duk a cikin wannan gidan mai”
Masu ruwa da tsaki akan wannan gidan mai sun bayyana cewa gidan man zai samar da aiyukan yi ga matasa a ƙalla sama da mutum ɗari, wanda hakan zai magance matsalar zaman kashe wando da matasan ƙasar nan su ke fama da ita.
Taron buɗe gidan ya samu halarcin mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ƴan majalisu, A.A Rano, Sarakunan Rano da Gaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan