Home / Labarai / Na Gamsu Da Shirin Buhari Akan Tattalin Arziki – Sarkin Kano Sanusi II

Na Gamsu Da Shirin Buhari Akan Tattalin Arziki – Sarkin Kano Sanusi II

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana cewar kasashen da ke mokobtaka da Najeriya ba sa taimaka mata wajen kare tattalin arzikinta.

Sarkin na Kano Muhammadu Buhari ya bayyana wa BBC cewar dole ce ta sa Najeriya ta dauki matakin rufe dukkan iyakokinta, domin ta bunkasa tattalin arzikinta musamman abin da ya jibanci noman shinkafa.

Hakan ne ya sa Sarkin yaba wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari kan matakin rufe iyakokin kasar daga shigar da abubuwan da ake iya samarwa a cikinta.

Sarki Sunusi ya kuma sake yaba wa Buhari dangane da kafa kwamitin kwararru domin kula da harkar tattalin arzikin kasar.


A baya dai Sarki Sanusi ya sha sukar gwamnatin Shugaba Buhari bisa gazawa ta fannin tattalin arziki.


Rahotan BBC Hausa

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Micheal Taiwo Akinkunmi: Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya cika shekaru 85 da haihuwa

A yau Litinin 10 ga watan Mayun shekarar 2021 mutumin nan da ya zama tutar …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *