Home / Labarai / Akwai Yiwuwar Gwamna Ganduje Zai Naɗa Tsohon Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Na Jihar Kano Kwamishina

Akwai Yiwuwar Gwamna Ganduje Zai Naɗa Tsohon Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Na Jihar Kano Kwamishina

Wata majiya daga fadar gwamantin jihar Kano ta bayyana mana cewa cikin ƙunshin mutanen da gwamna Ganduje ya ke shirin naɗawa a matsayin kwamishinoni akwai sunan tsohon shugaban ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano (NAKSS) wato Kwamared Ali Mai Kasuwa Rano.

Majiyar da ta buƙaci da a sakaye sunanta ta ƙara da cewa zaɓin da gwaman ya yi wa shugaban ɗaliban yana da nasaba da ƙoƙarin da gwaman ya ke yi na ganin ya yi gwamnati da matasa sababbin jini a ƙunshin sabuwar gwamnatinsa

“Gwamna Ganduje ya ƙuduri aniyar ganin wannan karon zai baiwa matasa dama a cikin gwamnatinsa, musamman ganin yadda su ka ba shi gudummawa a lokacin zaɓen da ya gudana”

Sai dai kuma wasu suna kallon rawar da Kwamared Ali Mai Kasuwa ya taka wajen sake zaɓen Gwamna da aka yi a zagaye na biyu, tare kuma da bayyana goyon bayansa ga Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Kawo yanzu dai tuni shiri ya yi nisa wajen tattara sunayen da gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai aiki da su a zagon mulkin jihar Kano karo na biyu.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

One comment

  1. Alhamdulillah Wanan Zabi Da Mai Girma Gwamna Yayi Akan Wanan Zakakurin Matashi Yayi Dai Dai Yin Hakan Shi Zai Kara Sawa Matasa Su Dara Acikin Wanan Gwamnati Mai Albarka Ta Dr Abdullahi Umar Ganduje A Zangon Mulki Na Boat

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *