Gobara Ta Ƙone Almajirai 26 A Ƙasar Laberiya

384

Akala dalibai 28 ne suka rasa rayukan su a wata gobara da ta kuno kai a wata makarantar islamiyya dake tsakiyar birnin Monrovia na kasar Liberia.
Tuni Shugaban kasar Georges Weah ya ziyarci wannan unguwa inda ya kuma jajintawa iyalan mamatan.
Mai magana da yahun fadar Shugaban kasar Solo Kelgbeh ya sheidawa kamfanin dillancin labaren faransa na AFP cewa sun samu bayanai da ke tabbatar da mutuwar mutane 28, masu kimanin shekaru kama daga 10 zuwa 20.
An fuskanci dandazo jama’a musaman iyayen dalibai da suka mamaye hanyoyin dake bayar da damar isa wannan makaranta, ida suka bukaci karin haske daga jami’an kai agaji dake kokarin tantace idan da sauren dalibai a cikin bene.
Rahoton farko da masu bincike suka aike zuwa fadar Shugaban kasar sun bayyana cewa gobarar ta riski daliban a daide lokacin da suke barci, kamar dai yada daya daga cikin shugabanin Fulani Amadu Sherrif ya sanar da masu binciken.
Shugaban kasar George Weah da kan sa ne ya ziyarci unguwar da gobarar ta faru ,inda ya kuma jajintawa iyayen daliben.

Ana ci gaba da samun rahotannin da su ke karo da juna dangane da yawan mutanen da suka rasa ran su, wasu na bayyana mutuwar almajirai 26, yayinda wata majiya ke bayyana mutuwar mutane 30.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan