JAMB Ta Dakatar Da Cibiyoyi 13 A Nasarawa

167

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ta dakatar da Cibiyoyin Rubuta Jarrabawa ta Komfuta, CBT Centres har 13 daga cikin 32 dake Jihar Nasarawa saboda rashin bin ƙa’ida.

Magatakardar Hukumar, Farfesa Ishaq Adeleye, ya bayyana haka a Gidan Gwamnatin Jihar Nasarawa dake Lafiya ranar Alhamis lokacin da yake sa hannu a kan wata Yarjejeniya Fahimtar Juna, MoU, da Hukumar Bunƙasa Ci Gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Nasarawa bisa samar da kayan aiki a Cibiyoyin Rubuta Jarrabawar ta Komfuta da Hukumar ta yi a wasu cibiyoyi uku mallakin Gwamnatin Jihar.

Mista Adeleye, wanda ya yi jawabi ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai, Fabian Okoro, ya ce: “Abin kaico ne a ce daga cikin Cibiyoyin CBT 32 a Jihar Nasarawa, mun dakatar da 13 daga cikin su.

Mista okoro ya ce: “Dakatarwar ta biyo ko dai rashin bin ƙa’ida ko wani abu, ko kuma matsayin bai kai yadda ake zato ba”.

Amma, ya bayyana fatan cewa da sa hannun JAMB a Yarjejeniyar Fahimtar Junan, MoU, da Gwamnatin Jihar, abin zai canza ta fuskar matsayin Cibiyoyin CBT a jihar.

“Amma abinda muke da shi a nan shi ne, wanda Gwamnatin Jihar ta haɗa kai da JAMB, shi ne ingantattun kayan aiki.

“Za ka iya tsayar da yawan ɗalibanka, kuma ka samu nutsuwa cewa jarrabawar za ta gudana cikin nasara ba tare da wata matsala ba”.

A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Sule ya yabi wanda ya gada, Sanata Tanko Al-Makura bisa yadda ya yi gine-gine a cibiyoyin da kuma tallafin JAMB na samar musu da kayan aiki.

A cewar Gwamman, “Zuba kayan aiki a cibiyoyin zai yaye wahalar da ɗaliban JAMB ke sha a jihar daga yin tafiya wajen jihar don rubuta UTME ɗinsu.

“Cibiyoyin uku za su fara aiki a UTME ta 2020, kuma za su karɓi ɗalibai daga Babban Birnin Tarayya, FCT, da sauran jihohin ƙasar nan”.

Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Ci Gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Nasarawa, Ibrahim Shehu, ya ce kamar yadda dokar JAMB ta buƙata na samar da komfutoci 25 masu jiran ko-ta-kwana a cibiyoyi 25, ɗalibai 2,350 za su iya yin UTME kowace rana a cibiyoyin uku.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan