Miji Ya Saki Matarsa Saki 3 Akan Kuɗin Kitso

42

Wannan mazaunin birnin Atlanta ne da ke kasar Amurka ya saki matarsa wacce suke zaune lami lafiya na tsawon shekaru bakwai, saboda abinda ya fada na cewa ya gaji da biya mata kudin kitso, kamar dai yadda takardun kotu suka bayyana.
Mutumin mai suna Jonathan Rhames ya bayyana cewa yana mutukar son matarsa tamkar ba zai iya rayuwa babu ita ba, amma kuma shi bai ga wani dalili da zai saka ya dinga fita yana wahala a wajen aiki ba, sannan a karshe ya dawo ya kawo mata kudin taje ta sanya gashi, gashin ma kuma na doki.
Mutumin ya ce: “Zai fi mini sauki mu sayi dokin sukutum in yaso sai mu dinga yakar gashin idan ya girma.
Sai dai wannan labari da aka wallafa shi a shafukan sadarwa na zamani, ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin mutane, in da kowa ke tofa albarkacin bakinsa, wasu na cewa bai kamata dama matar ta dorawa mijin alhakin komai ba, kamata yayi su dinga raba wahalar ita ma ta fita taje ta nemo kamar yadda yake fita yana nema.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan