Najeriya Na Gab Da Katse Lantarkin Da Ta Ke Baiwa Ƙasashen Nijar, Togo Da Benin

124

Ƙasashen Nijar Togo da Jamhuriyar Benin ka iya fuskantar karancin lantarki kowanne lokaci daga yanzu matukar basu dauki matakin biyan bashin wutar lantarkin da ƙasar nan ke binsu ba.
Tun da farko dai ƙasar nan na fuskantar matsalar wutar lantarki a wasu yankuna tsawon lokaci, yanzu haka an kafa wani kwamiti da zai gano abinda ya hana ruwa gudu a wannan fanni.
Sai dai bayan gudanar da binciken kwamitin ya bayyana cewa babbar matsalar da ke hana ruwa gudu wajen samarwa kamfanonin kasar nan wadataciyar wutar da zasu dogara bai wuce nauyin da ta ke dauka wajen bai wa wasu kasashen ketare lantarkin ba.
A cewar kwamitin kamfanin samar da lantarki na kasar Nijar Nigelec da kuma na Benin Ceb sun gaza biyan tarin basukan da ƙasar nan ke binsu wanda da kudaden za ta yi amfani wajen inganta bangaren lantarkin na ta.
Tun kafin yanzu dai, gwamnatin ƙasar nan ta yi barazanar katse lantarkin da ta ke bai wa kasashen 3 duk da sanadin tarin bashin da ta ke bin kasashen da suka gaza biya tsawon lokaci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan