OPay Ya Mayar Da Martani Game Da Garƙame Ofishinsa

OPay, kamfanin hada-hadar kasuwanci ta Intanet wanda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta garƙame ofishinsa bisa umarnin Gwamnatin Jihar Kano ya ce yana nan yana ƙoƙarin warware matsalolin da ya samu da Gwamanatin Jihar Kanon.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne jami’an ‘yan sanda suka yi dirar mikiya a ofishin na OPay, suka kuma kulle shi bisa zargin sa da rashin bin wasu ƙa’idoji da Gwamnatin Jihar Kano ta gindaya masa.

‘Yan sandan sun kori ma’aikatan kamfanin da kuma cincirindon direbobin A Daidaita Sahu dake wurin, waɗanda ke ƙoƙarin biyan kuɗin aikin da suka yi.

A wata sanarwa da Ridwan Olalere, Daraktan Aikace-aikacen na Kamfanin ya fitar a Kano ya ce OPay kamfanin ne mai rijista wanda yake son taimakon al’ummar Jihar Kano don su mori damar sufuri da kowa zai iya biya, ta hanyar amfani da ƙungiyoyin A Daidaita Sahu da gwamnati ta amince da su.

“Wannan ci gaba ne da maƙasudin buɗe ORide (wani reshe a manhajar OPay), wanda gurinsa shi ne ya mayar da sufuri ya yi sauƙi ga dukkan nau’in mutane a farashi mai rahusa. ORide yana da manufar samar da damammaki ta hanyar taimakon jama’a su je inda suke so daga inda suke”, in ji shi.

Ya bayyana cewa kamfanin, wanda ya fara ya fara aiki a Agusta, 2019, ya ba direbobin A Daidaita Sahu waya matsayin wani ɓangaren shirinsu yayinda yake ba su horo bisa yadda ake kiyaye kai da matakan tsaro kafin gwamnati ta gayyace shi.

“Yayinda muke ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa a cikin Gwamnatin Jihar Kano don gabatar da kamfanin, sai Gwamnati ta gayyaci OTrike don ya wayar mata da kai, ya kuma ilmantar da ita bisa tsarin kasuwancinsa haɗa da darussa game tsarin farashinsa, wanda abin mamaki ya yi ƙasa sosai, da kuma tantancewa da lasisi don fara kasuwancinsa’, in ji Mista Olalere.

Ya ƙara da cewa: “Da muka kammala tantancewar gwamnati, yanzu jihar ta aminta da kamfanin. An fara tattaunawar haɗa guiwa da kamfanin don samun warwarewar matsala daga OTrike don tsaftace sana’ar A Daidaita Sahu a Kano. Wannan shi yasa gwamnati ta buƙaci kamfanin ya saita kasuwancinsa don su yi dai-dai da dokokin kasuwancin jihar, yayinda KAROTA ke shirin fara yi wa direbobin A Daidaita Sahu rijista kwanan nan”.

Ya kuma ce al’ummar Jihar Kano “sun karɓi manhajar Intanet ta OPay hannu biyu-biyu”.

OPay wani kamfani ne dake ƙarƙashin Opera a Gungun Opera ta Intanet. An yi wa kamfanin rijista da sunan Paycom Nigeria Limited, ya kuma fara aiki a Agusta, 2018, da lasisin CBN a matsayin kamfanin hada-hadar ƙananan harkokin kuɗi ta hanyar jakarsa ta ajiya.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan