Yadda Aka Ci Zarafin Hoton Sarki Sanusi A Fadar Gwamnatin Kano

266

An sa hoton Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a ƙarshe a jerin hotunan Sarakunan Kano guda biyar Masu Daraja ta Ɗaya a Ɗakin Taro na Fadar Gwamnatin Jihar Kano, wato Coronation Hall.

Tun a 2014 ne tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya sa hoton Sarki Sanusi a Ɗakin Taron na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, lokacin da aka yi bikin naɗa shi a matsayin Sarkin Kano.

Hoton ya ci gaba da kasancewa a Ɗakin Taron har lokacin da gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi mulki a 2015, an kuma haɗa hoton Sarkin da na gwamna da na Shugaba Muhammadu Buhari.

To, sai dai biyo bayan takun saƙa da aka samu tsakanin Sarki Sanusi da Mista Ganduje, magoya bayan Gwamna Ganduje sun cire hoton Sarkin bayan da aka ayyana gwamnan a matsayin wanda ya lashe zaɓen 23 ga Maris.

A ranar Alhamis ɗin nan ne Gwamnatin Jihar Kano ta dawo da hoton Sarki Sanusi tare da na sabbin sarakuna huɗu da ta ƙirƙira, inda da aka sa hotunan a ciki da wajen bangon Ɗakin Taron.

Amma, an lura cewa hoton Sarki Sanusi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Kano an sa shi a ƙarshe a jerin hotunan sarakunan, abinda ya fusata wasu al’ummar Kano.

Yadda aka tsara hotunan ya nuna Aminu Ado Bayero- Sarkin Bichi a farko; sai Tafida Abubakar Autan Bawo, Sarkin Rano; Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya; Ibrahim Abubakar II, Sarkin Ƙaraye; sai Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano.

Ana ganin hakan dai a matsayin cin fuska, musamman tunda Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda Fadar Gwamnatin Jihar Kano take tana ƙarƙashin ikon Sarki Sanusi ne.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 8 ga Mayu ne Gwamna Ganduje ya ƙirƙri ƙarin masarautu a Jihar Kano tare da naɗa musu Sarakuna Masu Daraja ta Ɗaya, wani abu da ake ganin an yi shi ne don rage tasirin Sarki Sanusi.

Tun bayan zaɓen gwamnan Kano ne aka fara samun takun saƙa tsakanin Sarkin da Gwamna Ganduje, saboda zargin da Ganduje ke yi wa Sarkin cewa ya goyi bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf a lokacin zaɓen gwamna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan