GenCos Sun Saki Megawat 3,396 Na Wutar Lantarki

116

Kamfanonin Samar Da Wutar Lantarki, GenCos, da suka haɗa da kamfaninin samar da wutar lantarki ta gas da ta ruwa sun ce sun saki Megawat 3,396 na wutar lantarki ta ruwa a turken samar da wutar lantarki na ƙasa ranar Alhamis.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoton makamashi na kullum-kullum da Tawagar Bada Shawara Kan Wutar Lantarki a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ta fitar ranar Juma’a.

Rahoton ya ce wutar lantarkin da GenCos suka aika ta yi ƙasa da megawat 134.46 daga alƙaluman da aka fitar ranar Alhamis.

Amma, suka ce ba a iya samar da megawat 1,296.50 ba saboda ƙarancin iskar gas.

Rahoton ya lura da cewa haka kuma ba a iya samar da megawat 112.5 saboda rashin kayan rarraba wuta a lokacin.

Haka kuma, an kasa samar da megawat 2,521.40 saboda shi ma dai saboda ƙarancin kayan raba wutar.

A cewar rahoton, ba a samu asarar ko megawat ɗaya ba saboda ƙa’idojin huɗda da ruwa.

Rahoton ya ce ɓangaren wutar lantarkin ya yi asarar kimanin Naira Biliyan 1.9 saboda rashin isasshiyar iskar gas, rabawa da kayan tunkuɗa lantarkin.

Rahoton ya ce ƙololuwar megawat da aka samu ranar Alhamis shi ne 2,246.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan