Muna Jan Hankalin Gwamnatin Kaduna Akan Rushe Mana Coci – Kungiyar Kiristoci

167

Ƙungiyar mabiya addinin kirista reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yunkurin gwamnati na rusa cocin Anglican na Saint Geoges da ke Sabon garin Zaria, wadda aka gina a 1908.


An dai ce gwamnati na son rusa cocin ne da manufar fadada wata kasuwa da ke kusa da ita.


Shugaban kungiyar, Reverend John Hayab ya bayyanawa labarai cewa an sha yunkurin rusa majami`ar da nufin fadada kasuwar da ke makwabtaka da cocin ana fasawa saboda tarihinta.


“Yawancin wadanda suke shugabanci a yanzu ba a haife su ba lokacin da aka gina cocin”.


Reverend Hayab ya karyata cewa an bai wa cocin diyya “Muna zaune kawai sai muka ga wasika wai za a rushe coci saboda an biya kudin diyya. Ba bu wanda ya biya diyya”


“Na biyu wasikar kuma ba ta da kwanan wata a jikinta. Shi ya sa muke neman gwamnatin jihar ta Kaduna ta fada mana tana da masaniya kan wannan wasika idan ba haka ba kuma muna son ta hukunta duk mai hannu a al’amarin.”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan