Yunwa Na Barazana Ga Rayuwar Ƙananan Yara Sama Da Dubu 34 A Jihar Taraba

147

Yara kanana sama da dubu 34,000 ne ke fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon yuwana a jihar Taraba.


Jami’in hukumar tallafawa Ilimin ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya na jihar Bauchi Bhanu Pathak ya shaidawa manema labarai cewar rikicin manoma da makiyaya ya janyowa wa yara kanana dubu 34,419 fuskantar hatsarin yunwa.


Pathak ya kara da cewar sakamakon yadda babu isassun magunguna a yankin ba a iya kula da lafiyar yaran.


Ya ce “Idan gwamnati ba ta dauki matakin da ya kamata a kan lokaci ba to yaran na iya rasa rayukansu.”


Haka zalika ya kara da cewar akwai wasu yaran kanana dubu 75,000 da suke fuskantar zazzabi da maleriya sakamakon yadda babu maganin rigkafin cututtukan a yankin, kuma yara kusan dubu 500,000 ba sa zuwa makaranta a yankin.


Ana yawan samun mummunar arangama tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan