Liverpool Nacigaba Da Jan Zarensu Agasar Premier

33

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool naci gaba da jan zarensu a gasar ajin Premier ta kasar Ingila.

Hakan kuwa ya biyo baya ne bayan sun lallasa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a filin wasa na Stanford Bridge daci 2 da 1 a wasan mako na 6.

Ayanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Liverpool nada maki 18 daga wasanni 6 inda ta lashe wasannin gabadaya sannan sun jefa kwallaye 17 anjefamusu kwallaye guda 5.

Da alama idan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool taci gaba da tafiya ahaka zasu iya lashe gasar Premier duba da cewa sun lashe manyan kungiyoyin kwallon kafa guda 2 wato Arsenal da Chelsea duk da cewar ayanzu haka tazararsu maki 5 ne da Manchester City.

Shin ko Liverpool zasu lashe gasar duba da cewa suna yunwar kofin na Premier?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan