Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Ɗan Sheikh Ɗahiru Bauchi Shugaban SUBEB

239

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya naɗa ɗan shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Bauchi, Dakta Abubakar Ɗahiru Bauchi a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar, wato SUBEB.

Wata sanarwa da ta fito daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabi’u Mohammed Baba, ta ce haka kuma Gwamna Mohammed ya amince da naɗin Alhaji Yakubu Barau Ningi da Zakari Ibrahim a matsayin Manyan Kwamishinoni a Hukumar.

Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Yusuf Abdullahi Itas, Abbas Waziri da Comfort Audu.

Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan