Hukumar Hizba Ta Kano Ta Lalata Dubban Kwalaban Giya

124

Hukumar Hizba ta Jihar Kano ta lalata kwalaban giya dubu 196,400 da ta ƙwace a ƙwaryar birnin jihar.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fage ya sanya wa hannu.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan lalata kwalaban giyar a ƙauyen Kalemawa da yake cikin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ce Musulunci ya hana shan giya da ma dukkan abubuwa masu sa maye waɗanda ke iya kawar da hankalin mutum.

“A Musulunci, giya haramun ce.

“Ya kamata malamanmu na Musulunci, shugabannin addini da na al’umma su shiga a dama da su wajen kawo ƙarshen irin wannan baɗala”, a kalaman Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa dukkan sauran hukumomin Shari’a a jihar za su samu ci gaba da kulawa iri ɗaya daga Hukumar ta Hizba don ba su damar gudanar da aiki yadda ya kamata.

Sanarwar ta kuma jiyo gwamnan yana cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da tallafa wa Hukumar Hizba musamman bayan ƙaddamar da kuma sa anini ga dukkan kwamandoji a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

“Ina roƙon ku da ku ba su dukkan goyon bayan da ya wajaba don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata, hakan ba kawai zai haɓaka aikinsu ba ne, amma zai tabbatar da cewa al’ummarmu ta kuɓuta daga munanan laifuka”, in ji shi.

A jawabinsa, Kwamanda Janar na Hukumar Hizba ta Jihar Kano, Sheikh Haroon Ibni Sina ya ce hukumar ta yi nasarar hana siyar da giya da shan ta ƙarƙashin tanadin Sashi na 401 na Dokar Penal Code ta 2013 da kuma Dokar Shari’a ta Kano.

Ya ce kuma hukumar ta samu wani umarnin kotu da ya ba ta dama ta lalata motocin dakon giya fiye da 12 da ta ƙwace.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan