Yara 9 Sun Mutu Bayan Rugujewar Wata Makaranta A Ƙasar Kenya

157

Akalla ƙananan yara guda 7 aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata bayan rugujewar wani ginin makaranta a birnin Nairobin kasar Kenya.


Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Kenya Cyrus Oguna ya ce kawo yanzu gawar yara 9 su ke da ita, sai kuma karin wasu kananan yaran 57 da suka samu raunuka.


Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbin faduwar ginin ko da dai wasu na alakanta shi da tsufa ko kuma rashin inganci.


Yanzu haka dai masu aikin ceto na ci gaba da lalubo yaran da suka nutse a baraguzan gine-gine wadanda kawo yanzu ba a kai gano adadinsu ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan