Yawan Aure-Aure Ga Talakawa Na Haifar Da Talauci- Sarkin Zamfaran Anka.

97


Mai martaba sarkin Zamfaran Anka Alhaji Attahiru Muhd Ahmad ya yi kira ga masu karamin karfi ko rangwamen wadata su kaucewa auren mace fiye da guda daya.


Mai martaba Sarkin ya kuma bayyana damuwa kan yadda wasu ke yawan aure ko da ba su da halin rike ‘ya’yan da zasu haifa.


Ya kuma soki lamirin al’adar auri-saki da dake zama halayyar wasu mazan, inda ya alakanta ta da karuwar rashin tsaron da ke addabar jihohin arewacin ƙasar nan.


Sarki Attahiru Muhd Ahmad a wata zantawar sa da gidan radiyon BBC ya ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce “masu karamin karfi sun fi kowa yawan aure-aure alhalin sun san ba su da wadatar kula da iyali.”
Yace ”Ya kamata a rika yi wa mata da ‘ya’ya adalci, saboda yawanci za ka ga masu mafi kankantar albashi ke da wannan dabi’a.


“Za ka ga mai karamin albashin naira 18,000 yana da matan aure har uku da kuma wannan albashin yake tunkahon kula da su.”


“Akwai mai mace har hudu da ‘ya’ya 30, ta yaya zai iya kula da iyali? Idan ka bincika karshen ta ba shi ke kula da su ba”, in ji sarkin na Anka.


Haka kuma ya bayyana takaici kan maza masu dabi’ar auri-saki, ”akwai maza masu auri-saki, su auro mace da sun haifi ‘ya’ya daya ko biyu sai ya sake ta idan kuma za ta tafi da ‘ya’yanta ta ke tafiya.


“Ka ga anan babu batun ya kula da su, ba kuma lallai a ce yana musu aike ba,” in ji shi.


Wasu mata dai sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan wannan kira, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na cewa idan aka hana yawan aure-auren haka ba karamar matsala zai haifar ba sakamakon zawarawa sun yi yawa, wasu mazajensu sun mutu ko an kashe su.


Ba’a dai cika jin sarakunan arewa na fitowa bainar jama’a suna jan hakalin mutane game da yawan aurace-aurace ba, musamman ga wadanda ba su da halin rike iyali da tarbiyyantarwa.

Rahotan BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan