Za a yi Taron Ceto Kannywood Daga Durkushewa

245


Duba da yadda masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood) ta shiga a yan shekarun bayan nan, yanzu haka Moving Image Limited kamfanin da ya taba shirya babban taro don inganta harkar fim ya sake shirya gudanar da taron a karo na biyu.

Taron dai an shirya gudanar da shi ne daga ranar 27 Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba 2019, a babban Otal din nan na Bristol Place dake Kano, da zimmar habaka harkar fim da nemo kasuwa ga finafinan Hausa da aka yi su cikin Harshen Hausa da kuma hadaka gami da hadin gwuiwa don yin aiki tare.

An shirya bayar da horo ga wadanda suka yi rijista don samun kwarewa kan yadda ake fara shirya fim mai ma’ana tun daga tushe, da yadda ake gudanar da shi a wurin daukar bidiyo da kuma yadda za’a tace tare da kara masa kayan ado domin kayatarwa ga yan kallo.

Ana sanya rai baki daga sassan nahiyar Afrika da dama masu ruwa da tsaki a harkar fim zasu halarci taron da kuma yan Nigeria dillalan fina-finai mazauna kasashen waje.

Wani abin karin armashin kuwa shi ne akwai mukalolin da za a gabatar a wurin taron daga bakin manyan masu ruwa da tsaki a har kar fim da kuma malaman da suka karanci harkar daga makarantu.

Daga bisani kuma za a wallafa mukalokin da suka gabatar.Kuna iya tuntubarsu domin yin rijista ko karin bayani ta info@kilaf.org.ng ko ta (+234) 8035863023 ko kuma ku duba www.kilaf.org.ng

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan