Akwai Damarmakin Kasuwanci A Ɓangaren Noman Ƙasar Nan – Godwin Emefiele

202

Shugaban babban bankin ƙasar nan, Godwin Emefiele, ya ce akwai gagarumar damar bunkasa tattalin arziki a bangaren ayyukan noma na ƙasar nan.
Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, Godwin Emefiele ya ce akwai damarmaki a bangaren kiwon kifi, inda ya ce a yanzu, yawan kifin da ake samarwa a kasar ya tsaya kan ton miliyan 0.8 yayin da bukatar kifin ya tsaya kan ton miliyan 2.7, wanda ya samar da gibin ton miliyan 1.9.
Ya ce yanzu shirin bankin shi ne, hada hannu da gwamnonin jihohin dake yankunan teku domin su raya sana’ar kiwon kifi, da nufin cike gibin na ton miliyan 1.9 tare kuma da kawo ƙarshen dimbin kudin da ake kashewa na shigar da kifi daga kasashen waje.
A cewarsa, wannan gagarumar dama ce ta bunkasa tattalin arzikin jihohin ta hanyar samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari.
Har ila yau, ya ce an samu sauyi a ɓangaren noman auduga, kuma domin cimma sauyin, shirin bankin zai kunshi manoma 300,000 a jihohi 26 daga cikin 36 na kasar, a cikin wasu ‘yan shekaru masu zuwa.
Domin farfado da bangaren masana’antar sarrafa auduga da masaku da samar da sutura, bankin ya sa ido kan noman kadada 200,000 na ingantaccen auduga da aka rabawa manoma 200,000 a fadin kasar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan