Akwai ‘Yan Boko Haram A Zamfara- Gwamna Matawalle

151

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi zargin cewa da akwai ‘yan Boko Haram a Zamfara waɗanda wasu ‘yan siyasa suka ɗauka don su kawo tashin hankali a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Darakta Janar na Yaɗa Labarai, Yusuf Idris a yayin wani taron manema labarai ranar Litinin a Gusau.

Ya ce Gwamnatin Jihar: “Ta samu wasu rahotonnin sirri dake cewa wasu ‘yan siyasa marasa kishin al’umma ‘yan asalin jihar suna ƙulle-ƙulle don tayar da hankalin al’ummar jihar.

“Suna nan suna nufin cimma munanan buƙatun na ƙashin kai, suna haɗa baki da ‘yan Boko Haram don ƙaddamar da jerin hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, masu son zamam lafiya na jihar.

“Gurinsu shi ne su hargitsa zaman lafiyar da ake cin moriya yanzu sakamakon hanyoyin zaman lafiya da tattaunawa da gwamnati mai ci ta ɓullo da su.

“A cewar rahoton sirrin, waɗannan muggan mutane sun kammala shirye-shiryen ƙaddamar da hare-hare a ƙananan hukumomi bakwai na jihar.

“Haka kuma, suna son kai hare-hare a wasu muhimman wurare a cikin babban birnin jihar, kuma suna so su kawar da wasu muhimman mutanen jihar su biyu idan sun yi nasarar kai hare-haren.

“Ƙananan hukumomin da suke so su kai harin sun haɗa da Gusau, babban birnin jihar, Tsafe, Talata Mafara, Anka, Zurmi, Maru Maradun, muhimman wuraren da suke so su kai hare-haren kuma su ne Babban Masallacin Gusau da Gusau Mummy Market, inda suka san mutane na taruwa dare da rana.

“An ce an ɗauko hayar waɗannan ‘yan Boko Haram ne daga wurare masu nisan gaske don aiwatar da waɗannan munanan hare-hare da ake son fara kaiwa daga ranar Litinin, 23 ga Satumba zuwa 25 ga Oktoba”.

Gwamnan ya ƙara da cewa ya zama dole a ankarar da al’ummar jihar don hana mutane shiga ruɗu, a kuma yi bayani game da shirin gwamnati na haɗa kai da hukumomin tsaro wajen shawo kan matsalar.

Ya ce tuni an jibge jami’an tsaro a dukkan wuraren da ake sa ran samun hare-haren, yayinda ake ci gaba da kara wuraren binciken ababen hawa a dukkan sassan jihar.

Gwamna Matawalle ya nuna jin daɗi bisa fatan alheri da al’ummar jihar ke yi wa gwamnatinsa, ya kuma tabbatar da cewa: “Masu munanan manufofi ba za su hana shi ko takura masa ba a yunƙurinsa na inganta rayuwar jihar da al’ummarta”.

Gwamnan ya kuma gode wa mahara da suka tuba da ‘yan ƙungiyar ‘Yansakai bisa tabbatar da shirin zaman lafiya da gwamnatinsa ta ɓullo da ita, wadda ta kawo zaman lafiya a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito cewa jihar ta samu zaman lafiya a watanni biyu da suka gabata, inda masu garkuwa da mutane suka saki mutum 370 bisa raɗin kansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan