Mun Gamsu Sosai Da Rufe Bakin Iyakoki- Majalisar Dattijai

46

Majalisar Dattijai ta yaba da matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka na rufe bakin iyakoki ƙasar nan na ƙasa na ɗan wani lokacin don magance shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba da kuma irin tasirin haka a kan tattalin arziƙin Najeriya.

Wanna yabo ya zo ne bayan amincewa da wani ƙudiri mai taken: “Tasirin Rufe Bakin Iyaka Ga Tattalin Arziƙin Najeriya”, wanda Sanata Adamu Alero (APC, Kebbi ta Tsakiya) ya gabatar a zauren Majalisar ranar Laraba.

Majalisar Dattijan, a shawarwarinta, ta yi kira ga Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa da hukumomin tsaro da su ruɓanya ƙoƙari wajen daƙile shigo da kaya ba bisa ƙa’ida ba a dukkan iyakokin ƙasar nan, ta kuma tabbatar musu da goyon bayan Majalisar Dattijan a ƙoƙarinsu na raba Najeriya da kayayyakin da ake shigowa da su ba bisa ƙa’ida ba.

Da yake jagorantar muhawarar, Sanata Aliero ya ce: “Shigo da man fetur ba bisa ƙa’ida ba ya ragu sosai, abinda yasa ƙasar nan ta alkinta dubban biliyoyin daloli da da ma ba su wadata ba da Kamfanin Hada-hadar Man Fetur na Ƙasa, NNPC ke kashewa wajen shigo da man fetur Najeriya”.

Sanata Aliero ya lura da cewa shigo da tufafi da man girki da daga Malaysia ta bakin iyakokin ƙasar nan ya yi mummunan tasiri a yadda ake samar da su a gida ya kuma yi musu naƙasu.

“Matakin da Gwamnatin Tarayya ya haifar da dawo da samar da kayayyaki a gida kamar man girki, ya kuma ƙara samar da aikin yi”, in ji sanatan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan