Plateau United Sun Karbi Kayayyakin Wasa Karon Farko Daga Turkey

144

Kungiyar kwallon kafa ta Plateau United dage jahar Jos ta karbi kayayyakin wasa karon farko daga wani kamfani maisuna Kayspor da sukayi hadin gwiwa dashi daga kasar Turkiya domin fara buga sabuwar kakar wasa ta shekara ta 2019 zuwa 2020.

Daga cikin kayayyakin akwai riguna dauke da tamarin sunan kamfanin da kayan atisaye da manyan kaya na tafiya wasa da kwala-kwalai da safa da sauransu.

Kayayyakin dai an kswosu nan gida Najeriya a yau Laraba kuma tuni kungiyar kwallon kafan ta Plateau United ta karbi wadannan kayayyaki.

Jim kadan bayan karbar kayayyakin General Manager na kungiyar kwallon kafan wato Pius Henwan yayi magana kamar haka “nayi murna sosai ganin cewa mun karbi kayayyakin nan kuma kuma zamu karawa ‘yan wasanmu karsashi da masu horas warmu a sabuwar kakar wasa dazamu shiga.

Ina sa ran nan gaba kashi na biyu na kayayyakin wasan zasu iso Najeriya kafin afara sabuwar kakar wasa”

Henwan ya kara da cewa a nan gaba gwamnan jahar ta Jos wato Simon Lalong shine zai gabatar da kayayyakin da wannan kamfani ya turo da akayi hadin gwiwa a bikin budesu tare da bayyana sababbin ‘yan wasan da kungiyar kwallon kafan ta Plateau United ta dauka.

Ayanzu dai kungiyar kwallon kafan ta Plateau United ta cimma yarjejeniya da wannan kamfani na kasar Turkiya mai suna Kayspor cewar nan da shekaru biyu masu zuwa zai sake turomusu wasu kayayyakin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan