Tsakanin Kwankwasiyya Da Sheikh Pantami: Cin Zarafi Ba Sabon Abu Ba Ne – Bello Sharaɗa

119

Lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci fadar Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a harkokinsa na kamfen, a cikin tawagarsa har da Ambasada Aminu Bashir Wali.

Ambasada Wali yana cikin mutum 34 da suka kafa jam’iyyar PDP a 1998. Yanzu haka ma a kundin tsarin mulki na PDP an basu matsuguni na dindindin. Akalla ya shekara 50 yana siyasa, yana cikin dattijai da suka goyi bayan zaman Injiniya Rabiu Kwankwaso zama gwamna a 1999.

A ranar da aka je ziyarar Sarkin Kano duk da kasancewar Aminu Wali dan sarauta kuma dan siyasa a PDP amma babu wulakanci da cin zarafi da mutanen Kwankwasiyya basu yi masa ba. An cire masa hula, aka hana shi shiga fada, aka sanya masa jar hula. Laifinsa kawai ba ya yin Kwankwasiyya kuma yana da sabani da Kwankwaso.

Jiya a filin jirgin sama, mutanen Kwankwasiyya suka tare ministan harkokin sadarwa Dr Ali Isa Pantami. Sun yi masa tereren wulakanci da cin fuska har jar hula suka dora masa a tsakiyar kansa. Laifin Pantami ya soki kalmomin Kwankwaso akan tuhuma halittun Allah.

Ya kamata masu ra’ayin siyasa da wadanda suke yin siyasa kullum kullum, su gane siyasa ba rashin mutunci bane, ba kuma dirty game bane. Siyasa aikin al’umma ne, kuma jarumi da sadauki a cikin siyasa shi ne: mai hakuri da mutunci da bin ka’ida da tsari da girmamawa ga ra’ayin kowa koda ya saba da naka.

Irin wannan tsarin na Kwankwasiyya ba shi da albarka kuma ba gadon alheri bane. Malami zai iya shiga siyasa, Saraki zai iya shiga siyasa, dan kasuwa zai iya shiga siyasa, shigar mutum siyasa ba lasisi bane na iskanci da hauragiya da dabanci. TIR da irin wannan salon. Lokaci ya yi da malaman addini da sarakai da yan kasuwa masu daraja da girma da arziki da haiba da ilimi zasu dada shigowa cikin harkar siyasa da jam’iyya dumu dumu, su tsaya takarar mukami, su karbi mukami, sannan su rike jam’iyya. Babu zaman kallo ko dauke kai.

SIYASA BA RASHIN MUTUNCI BA CE,
AIKIN AL’UMMA NE
AIKIN AL’UMMA NA MUTANEN KWARAI NE
BA ‘YAN TASHA BA

Bello Muhammad Sharaɗa Ya Rubuto Daga Kano

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan