Wasu Miyagu Na Ƙoƙarin Damfarar Ƙasar Nan Biliyoyin Daloli – Shugaba Buhari

130

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, wasu miyagun kungiyoyin kasa da kasa na kokarin damfarar ƙasar nan biliyoyin kudade na Dala.


Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a zauren Majalsar wadda ke gudanar da taronta karo na 74 a birnin New York na Amurka.


Buhari ya bayyana yarjejeniyar huldar kasuwanci tsakanin kamfanin P&ID na Ireland da gwamnatin ƙasar nan a matsayin yunkurin wata damfarar ƙasar nan Dala biliyan 9.6.


Wata kotun Birtaniya ce ta bai wa ƙasar nan umarnin biyan maƙuden kuɗaɗen ga kamfanin na P&ID bayan wargajewar yarjejeniyar iskar gas da aka kulla tsakanin biyu a shekarar 2010.


Kamfanin ya cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin gina matatar iskar gas a jihar Cross River, amma yarjejeniyar ta tabarbare bayan shekaru biyu.


Kamfanin ya maka gwamnatin Najeriya a kotun birnin London akan zargin ta da karya ka’idojin yarjejeniyar.


A karon farko ke nan da shugaba Buhari ke tsokaci a bainar jama’a kan wannna batu wanda ya haifar da cece-kuce a ciki da wajen ƙasar nan.


Buhari wanda shi ne na biyar a jerin shugabannin da suka gabatar da jawabi a taron na Majalisar Dinkin Duniya, ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, yayin da ya caccaki kafafen sada zumunta saboda yadda ake amfani da su wajen yada miyagun ayyuka da tashe-tashen hankula da labaran karya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan