Za Mu Fara Gurfanar Da Masu Satar Wuta A Kotu- KEDCO

158

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO, ya gargaɗi masu yin zagon ƙasa ga kayan aikinsa, lalata tiransifoma, jan wuta ba bisa ka’ida ba, hana mita aiki da sauran laifuka cewa satar wuta ta kowane fanni babban laifi ne, kuma duk wanda aka kama da laifi, ya yi shirin fuskantar shari’a.

A wata sanarwa da jaridar Platinum Post ta samu, Shugaban Sashin Sadarwa na KEDCO, Ibrahim Sani Shawai, ya ce: “Sakamakon ƙarfafa sashinmu na shari’a da bincike na musamman da tawagar gurfanar da mutane gaban kotu a kan laifukan wuta waɗanda ake shiryawa don warware waɗannan matsaloli, kwanan nan masu lalata kayan wuta da ba su tuba ba da ɓarayin wuta za su san cewa abinda suke aikatawa babban laifi ne da zai iya jefa su a gidan yari na tsawon lokaci.

“Waɗanda ke da halayyar lalata transifomomin KEDCO za su iya fuskantar hukuncin shekaru 21 a gidan yari, ko hukuncin ɗaurin rai da rai yayinda tarar hana mita aiki za ta kai N50,000 zuwa N150,000. Satar wuta, jan wuta ba bisa ka’ida ba, rataye waya da cin zarafin ma’aikatan KEDCO duka laifuka ne da doka ta tanadi hukunci a kai.

“A cewar KEDCO, satar wuta, ko cuta ta hanyar mita, wadda wata hanya ce ta amfani da wuta ba bisa ka’ida ba, don a kasa auna ainihin wutar lantarki da aka yi amfani da ita babban laifi ne na tattalin arziƙi ko na kuɗi waɗanda ke da mummunan tasiri a kan KEDCO da abokan huɗɗarsa.

“To, duk wanda ke aikata haka ya sani cewa laifi ne da ba za a ci gaba da lamunta ba kwata-kwata, saboda an kammala shiri tsaf don fara fafata shari’o’i don ceto zuba jarin da KEDCO ya yi, mu kuma tabbatar da gamsuwar abokan huɗɗarmu.

“Waɗanda ke biyan ƙasa da abinda ya kamata su biya saboda mitarsu ta shiga matsala ko sun hana ta aiki su ma suna da laifin satar wuta”.

Daga ƙarshe KEDCO ya shawarci dukkan abokan huɗɗarsa da su kula da mitocinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan