Ƙungiya Ta Gano Sabon Shirin Ganduje Na Tsige Sarki Sanusi

235

Dattawan Kano ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna The Renaissance Coalition sun gano shirye-shiryen da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake yi na tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta gano cewa biyo bayan ƙirƙirar sabbin masarautu a jihar da kuma rage iko da tasirin Sarkin Kano, Sarki Sanusi ya daina halattar tarukan gwamnatin jihar.

An gano cewa Gwamnatin Jihar, ta zaɓi ta ƙulla kyakkyawar alaƙa da sauran sarakuna da ta ƙirƙiro, musamman Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero.

Majiyoyin cikin gida sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an shirya wata kutungwila ‘yan kwanakin da suka gabata na ‘mayar’ da Sarki Sanusi Bichi, a kuma rantsar da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.

“A fili yake cewa Sarki Sanusi ba zai karɓi canjin masarauta ya zama Sarkin Bichi ba. To, shirin shi ne, idan Sarki Sanusi ya ƙi yadda da haka, za su zarge shi da rashin biyayya sai su cire shi”, wata majiya da take da masaniyar yadda al’amura ke wakana ta faɗa wa DAILY NIGERIAN haka.

A halin yanzu dai Sarkin yana birnin New York, inda yake halattar Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya Karo na 74 tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Dattawan Kano Ba Su Yadda ba

A wata sanarwa da Ibrahim Waiya ya fitar ranar Alhamis ɗin nan, dattawan sun ce manufar shirin Gwamnan shi ne ya kawo tashin hankali a jihar maimakon ci gaba da zaman lafiya.

Sanarwar ta ce: “The Renaissance Coalition ta samu sanarwar cewa Gwamnatin Jihar Kano tana shirin canza Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sanusi II, CON zuwa Bichi, kuma idan ya ƙi zuwa, za a tsige shi.

“Wannan abin kaico ne, saboda duk da hukuncin kotu wanda ya umarci a koma yadda ake a baya har lokacin da za ta kammala sauraron ƙarar da aka shigar gabanta, da kuma dokar da aka yi cikin gaggawa don cimma wata mummunar manufa, kuma ake ƙalubalantar ta a kotu, ba ta bada damar yin irin wannan canjin ba.

“Wannan mataki ne mai haɗari sosai wanda zai iya kawo tashin tashina a siyasa, kuma wannan shirin da ake zargi ya nuna yadda Gwamnan ya kai maƙura wajen ciyar da buƙatarsa ta ƙashin kai gaba koda zaman lafiya da jin daɗin al’ummar da ya yi rantsuwar karewa za su shiga haɗari.

“Muna ganin haƙƙinmu ne mu yi dukkan wani abu mai yiwuwa cikin ikonmu wajen kira ga zaman lafiya da jin daɗin al’umma, ta hanyar yin kira ga dukkan mutanen dake son ci gaba da Gwamnatin Tarayya da su yi kira ga Gwamnan da ya dakatar tare da guje wa duk wani mataki da zai ƙara ɓata dangantaka ga Masarautar Kano da mutuncin Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sanusi II.

“Mun yi imani da karin maganar dake cewa maganin kar a yi, kar a fara, koyaushe mukan so mu kasance a tafarki madaidaici da kuma tafarkin tarihi madaidaici, mukan bayyana ra’ayinmu da ba son kai da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa don ɗaukar matakin da ya dace a kan lokaci don yin magance abubuwan da ka iya gurɓata al’umma.

“Mun yanke shawarar ba za mu jira muna kallo ba, za mu tashi tsaye ne, saboda nauyin tasirin da shirin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai yi ga al’ummar Kano, idan shirin da ake zargi ya kasance gaskiya, kuma ba a yi komai a kai ba.

“Saboda haka, a matsayinmu na ‘yan Kano da suka san abinda suke yi, kuma waɗanda abin ya shafa, muna kira da kakkausan lafazi ga Gwamnan da ya dakatar da aiwatar da wannan shiri da ake zargin sa da shi, da ma ire-iren waɗannan, waɗanda za su iya jefa ɗan zaman lafiyar da muke mora a jihar.

“Haka kuma, muna kira a keɓance ga hukumomin tsaro, shugabannin siyasa, dattawa, malamai masu girma, manazarta, jagororin al’umma da duk wani mutum ko mutanen da za su iya ganin gwamna da su ba shi shawara ya janye wannan shiri.

“Amma, idan Gwamnan ya ƙi amfani da wannan shawara mai kyau, ya je ya aiwatar da wannan mummunan ajanda, ba mu da zaɓi sai dai mu yi kira ga Gwamnatinn Tarayya da kakkausar murya da ta kafa dokar ta-ɓaci a Jihar Kano da zarar Gwamnan ya bada sanarwar wannan shiri da ake zargi don ceto Jihar Kano daga tasirin wannan mataki.

“Muna son yin amfani da wannan kafa mu tunatar da jama’a da Gwamnati bisa irin abubuwan da suka faru lokacin da aka yi yunƙurin ɗaukar irin wannan mataki a kan Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a 1981.

“Mun yi ƙarfin imanin cewa, a yau idan aka yi yunƙurin ɗaukar irin wannan mataki, zai zama mafi muni saboda ƙaruwar matsin zamantakewa da tattalin arziƙi waɗanda tuni sun harziƙa mutane, waɗanda a shirye suke a ga alamar su, da kuma ɗimbin matasa marasa aikin yi a jihar”.

Daga nan sai ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta ja wa Gwamna Ganduje kunne don ya dakatar da wannan shiri, “don tabbatar da cewa Kano ta ci gaba da zama lafiya”.

Lokacin da aka tuntuɓe shi, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya ƙi cewa komai game da batun.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan