Arewa Ta Na Bukatar Jagora Kamar Kwankwaso –Sheikh Khalil

300

An bayyana cewa, a halin da Arewa ta tsinci kanta a yanzu ta na bukatar jagororin da za a rika saurarar maganarsu kuma a yi aiki da ita kamar tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta kasa reshen jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, a zantawarsa da wakilinmu a Kano. Sheikh Khalil ya kara da cewa, babbar matsalar da yankin ke fama da shi a Najeriya a halin yanzu shi ne rashin jagora guda daya wanda zai jagoranci al’umma zuwa ga tudun mun tsira, ya na mai danganta wannan matsala da karancin girmama na gaba.

Ya ce, duk wanda a ka kawo a ka ce a saka shi gaba a matsayin shi ne jagoran yankin wanda za a rika girmama umarninsa, sai ka ga an rufar ma sa da sara da suka na batanci, ya na mai cewa hatta wanda ya kawo sunan jagoran shi ma ba zai tsira daga sharrin magauta ba, sabanin yankin Yarabawa da ke Kudu maso Yamma, wadanda a koyaushe su ke yin biyayya ga jagoransu a kan alkibla guda daya tun daga kan Awolowo har zuwa Tinubu.

A cewar shehin malamin, Arewa ma ta na da bukatar mutum irin Kwankwaso jajirtacce, mai gaskiya da amana, wanda ba ya yaudara kuma ya ke da cikakken tsarin da zai dore.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan