Ko Wane Hali Sowore Ke Ciki?

164

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙi sakin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore da take tsare da shi duk da karɓar takardar yin biyayya ga umarnin kotu da ta samu ranar Laraba da safe.

Marshal Abubakar, wani lauyan daga cikin lauyoyin Mista Sowore waɗanda Femi Falana ke jagoranta, ya shaida wa jaridar PREMIUM TIMES sun bar Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, SSS da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar Laraba ba tare da Mista Sowore ba.

Hakan dai na zuwa ne duk da umarnin kotu da ya ce a saki Mista Sowore ba tare da ɓata lokaci ba.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton yadda lauyoyin Mista Sowore suka miƙa takardun dake nuna lallai a yi biyayya ga umarnin sakin Mista Sowore a Ofishin SSS, inda wani jami’i, Ayuba Adam ya karɓi takardun da misalin ƙarfe 10.08 na safiyar Laraba.

Biyo bayan bayanin Mista Abubakar wanda ya bada hujjar yin biyayya ga umarnin kotun, lauyoyin Mista Sowore sun bar ofishin na SSS bayan sa’o’i 12 bayan da suka cika ɓangarensu na hukuncin kotu na 24 ga Satumba ba tare da SSS sun yi hakan ba.

Mista Abubakar ya ce jami’a SSS sun buƙace su da su dawo ranar Alhamis don “tattaunawa da Darakta Janar na SSS ɗin”, Yusuf Bichi.

Labari

A ranar Talata ne Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin sakin Mista Sowore ba tare da ɓata lokaci ba, wanda aka kama shi ranar 3 ga Agusta bisa shirya wata zanga-zangar juyin juya hali da aka yi wa laƙabi da #RevolutionNow.

An yi wannan zanga-zanga a wasu sassan Najeriya, duk da dai daga bisani jami’an tsaro sun dakatar da ita.

A ranar 20 ga Satumba, sai gwamnati ta tattara wasu laifuka guda bakwai da take zargin Mista Sowore da cin amanar ƙasa, almundahanar kuɗi da sauransu.

Bayan janye buƙatar neman ba Mista Sowore beli ranar Talata, sai lauya mai gabatar da ƙara, G. A. Agbdua, ya roƙi kotu da ta yi bayani ko: “saboda tsaron ƙasa”, za a iya ba Mista Sowore ‘yanci ko kuma a’a.

Mutane da dama da suka haɗa da wanda ya taɓa lashe Kyautar Nobel, Wole Soyinka sun caccaki Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da yadda take tafiyar da ƙarar Mista Sowore, da kuma yadda take ƙin bin umarnin kotu a mafi yawan lokuta.

Mista Soyinka yana mayar da martani ne ga zarge-zargen da ake yi wa Mista Sowore, yana mai cewa gwamnatin Buhari ta “kai wani matakin jin tsoro da ba a taɓa gani ba”.

An bada umarni da yawa na sakin tsohon mai ba Shugaban Jonathan Shawara Kan Tsaro, Sambo Dasuki, wanda aka kama tun a 2015, amma gwamnatin ba ta bi ba.

A kwanan nan ne Babban Jojin Najeriya, Ibrahim Tanko ya ce ba zai lamunci ƙin biyayya ga hukunce-hukuncen kotuna ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan