Samuel Eto’o Yayi Kakkausar Suka Akan FIFA

135

Tsohon dan wasan kungiyoyin kwallon kafan Mallorca da Madrid da Barcelona da Inta Milan kai harma da Chelsea kuma dan asalin kasar Cameroon wato Samuel Eto’o yayi kakkausar suka akan hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Inda Eto’o ya bayyana cewar hukumar kwallon kafan ta duniya tana nuna banbanci akan ‘yan wasan nahiyar Afrika wajen bayar da kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya wato World Footballer a shekaru bila adadin.

Eto’o ya kara da cewa yana tunanin lokaci yayi da yakamata suyi magana dangane da ‘yan wasan nahiyar Afrika.

Eto’o yace babu hanyar daza abi ace awannan shekarar babu dan wasan nahiyar Afrika acikin jerin ‘yan wasa 11 da hukumar kwallon kafan ta duniya ta fitar, domin acikin wadanda aka fitar Sadio Mane da Mohammed Salah sunfi wasu cancanta.

Sannan kuma ko a mutum 3 na karshe da sukayi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya babu Mane babu Salah alhalin dukkaninsu sun lashe gasar zakarun nahiyar turai sannan sun lashe gasar Super Cup bugu da kari sun lashe takalmin gasar ajin Premier data gabata.

Wannan kai tsaye za a iya cewa ana nuna banbanci akan ‘yan wasan nahiyar Afrika.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan